Rayuwata
Alhamdulillah!
"Wa'amma Bi-ni'imati Rabbika Fahaddis"
Ina godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki a bisa tarin ni'imomi da yayi min masu tarin yawa acikin rayuwata, waɗanda ba zan iya lissafa su ba, saboda yawan su ya wuce duk yanda nake tunani, wanda babu abun da zan ce da Ubangijina sai dai na kasance mai godiya a gare shi akodayaushe, tare da bin dokokin sa, da kuma bin umarnin sa acikin dukkanin al'amuran rayuwa ta..
Kaɗan daga cikin tarin ni'imomin da Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi min a rayuwa ta, waɗanda nake matuƙar alfahari da su akodayaushe su ne kamar haka;
-Ni'ima ta farko da Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi min ita ce, da ya halicce ni a cikin tsatson Musulunci gaba da baya, wanda nake bin tafarkin addinin Musulunci, tare da bin sunnar fiyayyen halitta Manzon tsira, Annabin rahama, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, wanda ba ni na tsarowa kaina kasancewa akan wannan tafarki ba, Ubangiji ne Ya ni'imta hakan a tare da ni.
-Ni'ima ta biyu da Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi min ita ce, sa'a da kuma dace da na yi da nagartattun iyaye, musamman mahaifina, wanda yayi ƙoƙari matuƙa sosai wajen kula da ni, da tsawatar min akan tarbiyya ta, da kuma ilimintar da ni, wanda na ke matuƙar alfahari da shi fiye da komai a rayuwata.
-Ni'ima ta uku da Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi min ita ce, da ya azurta ni da nagartattun ƴan'uwa, waɗanda tun tasowa ta suke ta faɗi tashi a kaina don ganin na zama cikakken mutum, wanda har kawo yanzu da na zama cikakken mutum babu wani abu da na nema na rasa daga gare su, wanda ya ƙunshi shawara, faɗa, nusarwa, tunatarwa, kyautatawa, kulawa da dai sauran su. Haƙiƙa wannan ma ni'ima ce babba a gare ni, wacce nake yiwa Ubangiji na godiya da ya bani ita.
-Ni'ima ta huɗu ita ce, damar samun ɗan ƙarami lilimi mai amfani da nayi, da kuma nasarar karanta ko'ina acikin Al-Qur'ani Mai girma da nayi, tare da karanta wasu ƴan tsirarun litattafai na Fiqhu da Hadisai, da dai sauran su. Wanda wannan ma wata ni'ima ce babba da Ubangiji Ya ba ni daga cikin ni'imomin Sa.
-Ni'ima ta biyar ita ce, kyakkyawar mu'amala da Allah Maɗaukakin Sarki Ya sa na ke yi da mutane, wanda har hakan ya janyo min alkhairai masu tarin yawa. Wanda ko kaɗan ba dabara ta, ko wayo na bane suka janyo hakan, Ubangiji na ne Ya ni'imta hakan a gare ni.
-Ni'ima ta shidda ita ce, ingantacciyar lafiya da Allah Maɗaukakin Sarki Ya azurta ni da ita, wanda a ni dai a tarihin rayuwa ta ban taɓa kwanciya akan gadon asibiti ba, har ta kai ga an ƙara min ruwa ko jini, ko wani abu makamancin haka. Sai dai ƙananan lalurori da ba a rasa duk wani ɗan adam da su ba. Haƙiƙa wannan ma ba dabara ta ko wayo na bane, Ubangiji na ne Ya ni'imta ni da hakan.
-Ni'ima ta bakwai ita ce, haɗuwa ta da wasu nagartattun mutane masu nagarta da tarbiyya, waɗanda suka ƙunshi manyan malamai, da zaƙaƙuran ɗaliban ilimi, da manyan ƴan kasuwa, da manyan ma'aikatan gwamnati, da manyan ƴan siyasa, waɗanda na haɗu dasu ta inda ban taɓa zato ko tsammani ba. Waɗanda da yawa daga cikin su na amfani ilimin su da alfarmar su a abubuwa daban daban. Wannan ma ni'ima ce da nake alfahari da ita.
-Ni'ima ta takwas ita ce, azurta ni da Allah Maɗaukakin Ya yi da wata salihar Mace, mai mutunci, mai ilimi, da nagarta, da kirki, da tarbiyya. Haƙiƙa kasancewa ta tare da ita akwai darasi, da wa'azi, da alfanu mai tarin yawa, wacce nake fatan kasancewa tare da mai irin halin wannan baiwar Allah a matsayin abokiyar rayuwa ta.
-Nasarori masu tarin yawa, da jarrabawar rayuwa mai tarin yawa, da sauran ƙalubale masu tarin yawa, su ma waɗannan duk wasu ni'imomi ne a gare ni da nake matuƙar alfahari da su, na ke kuma yiwa Ubangiji na godiya akan su.
-Kasancewa ta a ƙarƙashin jagoranci da shugabancin baba na mai martaba sarkin Kazaure, Alh. (Dr) Najib Hussaini Adamu, CON, haƙiƙa ita ma wannan wata ni'imace a gare ni wacce nake alfahari da ita, musamman idan na yi duba da irin tarin alkhairan mai martaba sarki a gare ni, da kuma irin alfarma da yayi min a abubuwa da yawa, wanda wayo na, ko dabara ta ba za su sa yayi min hakan ba.
A ƙarshe babu abun da zan ce da Allah Maɗaukakin Sarki wanda ya wuce na ci gaba da yin godiya a gare Shi, saboda ya azurta ni da abubuwa masu tarin yawa, wanda wayo na, da dabara ta duk ba su isa su sa na same su ba. To ina roƙon Sa da ya ci gaba da sanya albarka da alkhairi da ni'imomin Sa acikin sauran abun da ya rage min na rayuwa ta, Amin.
Daga;
Adamu Kazaure!
Comments
Post a Comment