Komai ya yi farko zai yi ƙarshe

Rayuwa kenan. A lokacin da na kammala karatu ba ma kowa nake ɗaukar wayar sa ba, saboda a lokacin ina matuƙar ji da kaina, ni kawai a tunani na ai na zama wani fitacce. Ko da chatting muke yi da mutum, to fa zai ga ƙaryar turanci, a dole wai ni ga ɗan boko, bayan kuma ɗan turancin na wa ma bai fi cikin cokali ba.

To amma fa daga lokacin da duniya ta sako ni a gaba, 1k ta ringa burgeni tare da bani sha'awa, saboda ba ni da wanda ina zaune zai bani ita, to a sannan ne fa na ƙara fahimtar dalilin da yasa taken Nijeriya ya ƙare da "So help me God" saboda a lokacin ban da taimakon Allah Ta'ala babu abun da nake nema. A wancan lokacin duk wani portal na bayar da tallafi ko na aiki da aka buɗe, to fa sai da na cike shi. Na halarci screening da interview ya yi sau Goma ba tare da na samu ba, amma duk da haka ban sare ba, na ci gaba da cikewa duk bana samu. 

Da ƙyar na samu Npower a shekarar 2016, inda aka tura ni wani Primary Health Care da ke wani ƙauye, wanda ni dai tunda nake a rayuwa ta wallahi ban taɓa zuwa wannan ƙauyen ba. Da ƙyar dai na samu na baro wannan ƙauye na dawo cikin gari domin gudanar da wannan aiki na Npower. Bayan kammala aikin Npower cikin iko da taimakon Allah Maɗaukakin Sarki sai abubuwa suka fara buɗewa, alkhairi iri-iri ya ringa zuwa gare ni ba tare da na yi tsammanin sa ba, wanda kawo yanzu babu abun da zan ce da Ubangiji sai dai kawai na yi godiya a gare shi. Alhamdulillah, tabbas komai me wuce wa ne, musamman ma idan aka yi haƙuri, saboda duk tsananin wuya, to fa sauƙi yana nan tafe. Amma ko a yanzu Allah Ta'ala Ya halicce ni, ya kuma ce na tsarawa kaina komai, wallahi ba zan iya tsarawa kaina irin tarin ni'imomin da yayi min ba a yanzu.

To wani darasi da nake so na ba ƴan'uwana matasa shi ne, ko da wasa kar ku sake ku dogara kawai da Degree, ku tashi ku nemi sana'a duk ƙanƙantar ta, wadda za ku rufawa kan ku asiri da ita. Dogaro da hanyar samun kuɗi guda ɗaya tak a wannan yanayi da muke ciki kuskure ne babba, musamman ma idan hanyar samun ƙarama ce. Ni dai akoda yaushe ina yawan faɗan cewa ɗaya daga cikin manyan danasani da na taɓa yi acikin rayuwa ta shi ne rashin koyon sana'a tun da wuri. Kawai na tsaya jiran sai Gwamnati ta bani aiki, wanda hakan kuskure ne babba.

A ƙarshe ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ci gaba da rufa mana asiri, Ya kuma ci gaba da yi mana jagoranci acikin dukkanin al'amuran rayuwar mu, Amin.

Ɗan Almajiri.

Comments

Popular posts from this blog

Who is Adamu Kazaure?