Rayuwata

Alhamdulillah! "Wa'amma Bi-ni'imati Rabbika Fahaddis" Ina godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki a bisa tarin ni'imomi da yayi min masu tarin yawa acikin rayuwata, waɗanda ba zan iya lissafa su ba, saboda yawan su ya wuce duk yanda nake tunani, wanda babu abun da zan ce da Ubangijina sai dai na kasance mai godiya a gare shi akodayaushe, tare da bin dokokin sa, da kuma bin umarnin sa acikin dukkanin al'amuran rayuwa ta.. Kaɗan daga cikin tarin ni'imomin da Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi min a rayuwa ta, waɗanda nake matuƙar alfahari da su akodayaushe su ne kamar haka; -Ni'ima ta farko da Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi min ita ce, da ya halicce ni a cikin tsatson Musulunci gaba da baya, wanda nake bin tafarkin addinin Musulunci, tare da bin sunnar fiyayyen halitta Manzon tsira, Annabin rahama, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, wanda ba ni na tsarowa kaina kasancewa akan wannan tafarki ba, Ubangiji ne Ya ni'imta hakan a tare da ni. -Ni'ima ta biyu...